Fada ya kaure tsakanin kungiyoyin ‘yan tawaye a Somaliya

0
50
'Yan tawayen Somaliya

Jami’ai sun bayyana cewa akalla mutane ashirin da tara ne suka rigamu jidan gaskiya yayinda fiye da hamsin suka jikkata sakamakon fadan da ya kaure tsakanin ‘yan tawaye a gundumar Galkayo dake yakin tsakiya Somaliya.

Tun dai a ranar lahadin da ta gabata ne rikicin ya kaure tsakanin yankunan Puntlanad da Galmudug masu kwarya-karyar cin gashin kansu, sakamakon wata takkada dake da nasaba da tsare tsaren gina gidaje.

Wani jami’in sojan Puntaland, kanal Muhammed Aden ya bayyana cewa an kashe sojojin shida yayin da talatin daga ciki suka jikkata.

Rahotannai sun bayyana dukkanin bangarorin ‘yan tawayen biyu na mara wa gwamnatin Somaliya baya wadda a gefe guda ke samun goyon baya daga majalisar dinkin duniya.

 

Abdulkarim/Shu’aibu

SHARE

NO COMMENTS

LEAVE A REPLY