FIFA ta nada Dan Najeriya a cikin kwamitin daá

0
43

Hukumar Kwallon kafa ta duniya (FIFA) ta nada alkalin alkalan kotun Jihar Legas, mai sharia Ayotunde Phillips a cikin kawamitin ta na da’a a ranar alhamis.

Wannan ba karamin ci gaba  ba ne ga Najeriya idan aka yi la’akari da cewar zai kasance al’kali na farko a Najeriya da hukumar kula da Kwallon kafan ta duniya da nada, kana wata dama ce ga ci gaban kwallon kafa a Nahiyar Afrika.

A halin yanzu taron shugabannin kungiyar FIFA da ya gudana a birnin Manana na kasar Bahrain ranar Alhamuis, ya tabbatar da zaben Shugaban Hukumar zaben Jihar Legas, mai sharia Phillip a matsayin mamba a Kwatin daa na Hukumar ta FIFA. Wannan shi ke nuna alamun daga martabar Najeriya a fagen kwallon kafa na kasa da kasa.

Vassilios Skouris daga kasar Girka ne ke jagorancin Sabon kwamintin da’ar na hukumar FIFA, yayin da tsohon Antoni janar na Amurka Samoa yake a matsayin mataimakinsa.

Sauran Mambobin Kwamitin sun hada da Muhammada Ali Al kamali (daga daular Larabawa), da Aivar Pohlak( dan kasar Estoni dake Nahiyar Turai), sai Margarita Echeverria (daga Costa Rica), da Jack Kariko (daga kasar Guinea) da Kuma Flavio Zveiter (daga Barazil).

 

Abdukarim Rabiu