Kwara United ta Lashe kofin Kalubale na Wannan Shekarar

0
47

Kungiyar kwakllon kafar wadda ake yi wa lakabi da Harmony Boys ta lallasa takwararta ta ABS Ilorin da ci 1-0 a wasan karshe da suka kare a yammacin ranar Asabar a garin Ilorin babban birnin Jihar Kwara.

Bayan dawo wa daga hutun rabin lokaci dan wasan gaba da a ka fi sani da Bishop na Kwara United ya zura kwallo a ragar ABS Illorin.

Mutane da dama ne dai suka je kwallon wasan na karshe, ciki kuwa har da Kwamishinan wasanni da ci gaban matasa, Kale Ayo, da shugaban Hukumar Kwallon kafa ta Jihar, Busari Ishola.

 

Abdulkarim Rabiu