Najeriya: Jihohi 10 ne zasu faffata a gasar Lig ta kwallon gora

0
48

A kalla jihohi goma ne zasu fafata a gasar Lig ta kasa na Kwallon Gora a filin wasa na kasa dake Abuja babban birnin Najeriya, Farawa a ranar Litinin din nan.

Babbar sakatariyar kungiyar Kwallon gora ta kasa a Najeriya Rita Akande, ta ce za a kammala gasar a ranar 20 ga watan Mayu, ta kara da cewa wadanda suka yi nasarar cin gasar zasu sami karin girma zuwa babban kungiyar wasan kwallon gora ta kasa.

Babbar Sakatariyar ta ayyana Jihohin Delta, da Bauchi, da Nassarawa daga cikin jihohin da zasu faffata a gasar Lig din.

Akande tace, ”Za a faffata sosai a gasar lig din saboda ko wannensu yana so ya samu damar shiga kungiyar Kwallon gora ta kasa. Duka kungiyoyin a shirhye suke domin faffatawa a gasar, da zimmar neman samun karin girma.’’

Har ila yau sakatariyar ta ce wasu kungiyoyin kwallon gora na mata zasu fafata a garsar lig din.