Najeriya: An Cafke Wasu ‘Yan Boko Haram A Nassarawa

0
37
Hukumar Tsaro Ta Farin Kaya A Najeriya, DSS

Rundunar tsaron farin kaya DSS, a Najeriya ta cafke mutum biyu da take zargi da ayyukan ta’addancin Boko Haram a kauyukan Amba da Gudi na jihar Nassarawa arewa ta tsakiyar kasar.

Wadanda ake zargin su ne Ibrahim Mala da kuma Abdullahi Modu wadanda ‘yan asalin jihar Borno ne da suka gudo sakamakon matsin lambar sojoji kana suka saje cikin al’umma.

A jawabinsa, wani jami’in rundunar Mr. Tony Opuiyo ya bayyana cewa daya daga cikin mutanen Abdullahi Modu mai sana’ar sayar da tufafin yara ya tabbatar masu da cewa yana da alaka da Boko Haram, in da ya ce Ibrahim Mala wanda yake sayar da turare ya shiga kungiyar Boko Haram a shekarar 2017.

A wani labarin daban, Mr. Opuiyo ya tabbatar da cafke Abdulkarim Dahiru dan asalin jihar Kogi dake zaman gagarumin dan ta’adda a asibitin kwararru ta jihar Legas.

Haka kuma hukumar tsaron ta cafke jagoran ‘yan Boko Haram na garin Okene a jihar Kogi, Abdullahi Muhammed.

Da man dai rundunar ta sha alwashin gudanar da ayyukan ta na zakulo masu aikata ta’asa a duk inda suke.

 

Shuaibu Nasiru

NO COMMENTS

LEAVE A REPLY