Dakarun Tsaro Zasu Goyi Bayan Kwamitin Shugaba Buhari

0
30
Shugaban Rundunar Tsaron Najeriya, Janar Abayomi Olanisakin

Rundunar tsaron Najeriya ta bayar da tabbacin goyon bayanta ga kwamatin zaman lafiya da shugaba Muhammadu Buhari ya kafa akan yankin arewa maso gabashin kasar.

Shugaban rundunar tsaron kasar, Janar Abayomi Olanishakin shi ne ya tabbatar da hakan yayin da manbobin kwamitin suka ziyarce shi a ofishinsa dake birnin Abuja.

Shugaban rundunar tsaron wanda ya samu wakilcin Iya-bayis Bashir Sai’du inda ya bayyana cewa a shirye rundunar tsaron take ta hada kai da kwamitin ta kowacce siga da nufin tunkarar kalubalen da ‎’yan gudun hijira ke fuskanta a yankin, tare da gaggauta sake gina masu muhalli.

“Abin bukaci a nan shi ne samun hadin kai tsakanin sojoji da wannan kawamiti, har sai an cimma buirn da aka sa a gaba cikin nasara”. In ji shi.

Tun da fari, mataimakin shugaban kwamitin Alhaji Tumsa yabawa sojojin ya yi a bisa namijin kokarin da suka nuna wajen fatattakar ‘yan Boko Haram a dajin Sambisa.

Sannan ya kara da cewa wannan ziyara ta su na matsayin bayyana wa rundunar tsaron kasar shirin da kwamitin su yake yi dangane da aikin da ke gabanshi.

 

Shuaibu Nasiru

 

NO COMMENTS

LEAVE A REPLY