Kasar China Zata Kara Zuba Jari A Najeriya

0
41
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da Ministan harkokin Wajen Kasar Sin, Wang-Yi a Abuja

Ministan harkokin wajen kasar Sin, Wanga Yi na gudanar da ziyara a Najeriya da nufin kara inganta huldar kasuwanci da zuba jari a kasar.

Mr. Yi ya samu tarbar ta musamman daga babban sakataren ma’aikatar harkokin wajen Najeriya Ambasada Sola Enikanolaiye a filin jirgin saman kasa da kasa na Nnamdi Azikiwe dake babban birnin tarayya Abuja ya kuma bayyana cewa akwai kimanin jari na dalar Amurka miliyon dubu arba’in da kasarsa zata zuba a Najeriya.

Ministan harkokin wajen kasar ta Sin zai kwashe kwanaki shida a ziyarar da ya kawo ma Najeriya da kuma wasu kasashen Afrika.

Wanna ziyar ana kwautata zaton cewa zata yaukaka huldar kusawanci tsakanin kasarsa da kuma nahiyar Afrika.

SHUAIBU

NO COMMENTS

LEAVE A REPLY