Najeriya Ta Baiwa ‘Yan Kasashen Ketare Izinin Dan Kasa

0
14
Abdurrahman Danbazau, Ministan harkokin cikin gida a Najeriya

Majalisar zartarwar Najeriya ta amince da baiwa ‘yan kasar waje 300 izinin zama dan kasa, yayin da ta ki amincewa da mutum 165.

Ministan harkokin cikin gida a kasar, Janal Abdurrahman Danbazau mai ritaya, shi ne ya sanar da hakan yayin zantawarsa da masu aiko da rahotanni daga fadar gwamnati a Abuja, babban birnin kasar.

Inda ya bayyana cewa kwamitin kula da sha’anin zama dan kasa na ma’aikatun gwamnatin tarayya ya karbi takardun masu neman izinin zama dan ‘yan kasa su 500 kana kuma bayan sun tantance suka amince da mutum 335.

Ministan ya kara da cewa wadanda suka yi nasarar su cika ka’idar dake kunshe a cikin sashe na 26 da kuma na 27 na kundin tsarin mulkin kasar.

 

SHUAIBU

NO COMMENTS

LEAVE A REPLY