Shugaba Buhari Ya Halarci Ratsar da Shugaban Kasar Ghana

0
28

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bi sahun takwarorinsa wajen halartar rantsar da sabon shugaban kasar Ghana Mr. Nana Akufu-Addo da mataimakinsa Muhamudu Bawumia a birnin Accra na kasar.

Inda shugaba Buhari ya taya al’ummar kasar murnar gudanarda zabe cikin lumana gami da mika mulki cikin ruwan sanyi ga sabon shugaban.

Buhari ya kuma yaba wa tsohon shugaban kasar John Dramani Mahama kan yadda ya nuna dattako.

Bayan kammala rantsuwar shuwagabannin kasashen yammacin nahiyar Afruka suka tattauna matsayinsu kan shugaban kasar Gambia Yahya Jammeh da yaki amincewa da kayen da ya sha a zaben da a aka gudanar a kasar.

 

Shuaibu Nasiru

NO COMMENTS

LEAVE A REPLY