Enugu Rangers Ta Samu Kayyakin Wasa

Nura Muhammed, Abuja

0
32
Gwamna Jihar Enugu yayin da yake karbar kayayyaki

Manajan ‘yan wasan kungiyar kwalon kafa ta Manchester City dake kasar Ingila Keleche Iheanacho, Kingsley Ogbodo ya mikawa kungiyar kwalon kafa ta Enugu Rangers dake zama zakaran wasan premier league na Najeriya a kakar wasan bara.

A cewarsa, ya yi hakan ne domin ya karfafa ma su a yunkurinsu na tunkarar wasanin Premire da na zakarun nahiyar Afrika.

Gwamnan jihar Enugu dake kudu maso anashin kasar, Ifeanyi Ugwuanyi shi ne ya karbi kayayyakin a madadin kungiyar, ya kuma yabawa wadanda suka bada kayayyakin inda ya ce hakan zai taimakawa kungiyar samun nasara a wasanin ta a nan gaba.

Shuaibu Nasiru

NO COMMENTS

LEAVE A REPLY