Rivers Da Enyimba An Tashi Chanjaras

Nura Muhammed, Abuja

0
14
Wasan sada zumunci: Fafatawar Enyimba da Rivers

Manyan kungiyoyin wasanin kwallon kafar Najeriya Enyimba da Rivers United sun tashi wasa chanjaras 0-0 a wasan sada zumunci da kungiyoyin biyu suka yi na neman share fagen fara gasar wasanin Premier League na kasa.

Tun da fari dai, kungiyar Rivers United ce ta mamaye wasan har tsawon mintuna 35. Sai dai daga baya ‘yan wasan Enyimba suka taso inda suka hana Rivers sakat.

Sai dai mahuntan kungiyar Rives sun yaba da was an, inda suka ce hakan  ya sanya su samun kwarin gwiwa a wasannin da zasu buga musamman a gasar cin kofin zakarun nahiyar Afrika.

 

Shuaibu Nasiru

NO COMMENTS

LEAVE A REPLY