An rantsar da Sabon Shugaban Kasar Ghana 

0
16

Shugaba Nana Akufo-Addo mai shekaru 72 da haihuwa ya sha rantsuwar kama aiki a matsayin shugaban kasar Ghana na 12 kana kuma na biyar a jamhuriya ta hudu.

Shugaba Nana Addo ya sha rantsuwa ne a Accra babban birnin kasar a safiyar asabar din nan.

Sabon shugaban ya sha alwashin rage kudin haraji gami da yakar cin hanci da rashawa da kuma samar da ayyukan yi ga al’umma.

Haka kuma shugaban ya yi alkawarin bayar da ilimi kyauta ga ‘yan kasar tare da farfado da masana’antun da suka durkushe.

Shugaba Nana Akufo-Addo dan jam’iyyar New Patriotic Party mai adawa a kasar. Kama kuma kwararren lauya ne mai fafutukar kare hakkin bil adama.

A baya dai karo biyu yana shan kaye a takarar shugaban kasar gabanin samun nasara a wannan karon.

Wasu shuwagabannin kasashen Afirka sun samu halartar rantsuwar, ciki har da shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya.

Shuaibu Nasiru

NO COMMENTS

LEAVE A REPLY