An Gano Fasinjojin Jirgin Venezuela Kwanaki Shida Da Ya Bata

0
13

Rahotanni daga kasar Venezuela na nuni da cewa masu aikin ceto sun gano fasinjojin jirgin helikofta na sojoji da ransu bayan da aka shiga kwana na shida da jirgi ya yi batan dabo.

Mutane goma sha uku ne ciki har da fararen hula yayin da jirgin ya yi sama ko kasa a ranar Alhamis din makon jiya.

Masu aikin ceto na shawagi
Masu aikin ceto na shawagi

Wata majiya ta bayyana cewa sojojin dake cikin jirgin ba su mutu ba kuma za a mika su babban birnin jihar Amazonas, Puerto Ayacucho.

Sai dai kuma babu tabbacin ko fararen hular dake cikin jirgin suna raye.

Wasu mutanen daji ne dai suka gano jirgin a cikin tsaunuka kamar yadda gwamnan jihar ta Amazonas ya sanar.

An dai zargi gwamnatin kasar da nuna rashin cikakkiyar kulawa wajen aikin ceton.

 

Shuaibu Nasiru

NO COMMENTS

LEAVE A REPLY