Rikicin Kabilanci: An Kafa Dokar Ta-Baci a Kafanchan

0
131
An Sha Samun Rikicin Kabilanci a Kudancin Kaduna

Karamar hukumar Jama’a dake jihar Kaduna arewa maso yammacin Najeriya ta ayyana dokar ta-baci a garin Kafanchan da kewaye da nufin dakile aukuwar rikici a yankin.

Dokar ta ba shiga ba fita, an kafa ta ne Litanin din nan, biyo bayan zanga-zangar lumana da matasan garin suka gudanar a bisa kisan mutane da ake yi a yankin kudancin Kaduna.

Shugaban riko na karamar hukumar Dr. Bege Katuka ya tabbatar da wannan labari yayin da aka tuntube shi ta wayar tarho.

Dr. Katuka ya ce wannan mataki ya zama wajibi domin gujewa barkewar rikicin da ka iya sadanin rayuwa da dukiyoyin al’umma.

Daga karshe ya shawarci mazauna yankin da su kwantar da hankulansu kana zauna a gida har sai abin da hali ya yi.

 

Shuaibu Nasiru

NO COMMENTS

LEAVE A REPLY