Dakarun Syria Na Kara Kutsa Kai A Birnin Aleppo

0
29
Gidajen da aka lalata a wata unguwa a gundumar Sakrour

Bayan wata fafatawa tsakanin dakarun sojin kasar Syria da ‘yan tawayen kasar, dakarun gwamnatin sun kuma kwace iko da gundumar Sakhour mai matukar muhimmaci a gabashin birnin Aleppo.

Kungiyar kare hakkin bil Adama da kuma gidan talabijin na kasar sun tabbatar da faruwar al’amarin.

A baya dai a cikin watan Satumba, dakarun kasar suka kaddamar da wani farmaki da nufin kwace iko da birnin Aleppo, inda aka shafe makonni ana gwabza kazaminfada, lamarin da ya haifar da tserewar daruruwan fararen hula daga yankunan dake hannun dakarun ‘yan tawayen.

Rahotanni sun bayyana cewa a kasar ta Syria fada na ci gaba da kazanta a kasar tun fiye da shekaru biyar da suka gabata.

Inda hukumar kula da kananan yara ta majalisar dinkin duniya UNICEF ta koka kan yadda kai agaji a wasu yankuna kasar ke naman zama babban kalubale.

 

Shuaibu Nasiru.

 

NO COMMENTS

LEAVE A REPLY